SOKOTO, NIGERIA - Wannan na zuwa ne lokacin da rundunar ta ke samun kwarin gwiwa daga wasu gwamnatoci a kokarin ta na samar da tsaro a Najeriya.
Bayanan da ke fitowa daga wasu sassa na Najeriya sun nuna cewa ‘yan bindiga na zafafa kai hare-hare ga jama'a kwanannan musamman a wasu yankunan arewa maso yammacin kasar.
Jihar Sakkwato na daga cikin wuraren da ‘yan bindigar suke kai hari ga jama'a, inda a kasa da mako daya an sami kai hare-hare da satar mutane a yankuna da suka hada da Kware, Illela, Gwadabawa, Sabon Birni, Wurno da Isa inda jama'a ke ta kokawa.
Damuwa da sake bullar matsalar ne musamman a karamar hukumar Tangaza ya sa rundunar sojin Najeriya ta ce ba za ta saka ido ana yi wa jama'a kisan gilla ba.
Shugaban yanki na 8 na rundunar sojin Najeriya mai hedikwata a Sakkwato Manjo Janar Godwin Mutkut ya ce tuni sun soma aikin dakile ayyukan ‘yan bindigan.
“Ya ce bamu ji dadin faruwar hakan ba, kuma zuwa yanzu mun fara aikin farautar wadanda suka yi wannan aika-aika kuma ba da jimawa ba zamu kamo su, su girbi ladar aikin da suka yi. Hakika mun ji ciyo gaya akan faruwar wannan abu inda muke da ikon magance faruwarsa"
Gwamnan Sakkwato Ahmad Aliyu ya ce gwamnatinsa a shirye take ta bayar da cikakken goyon baya ga rundunar sojin.
“Ya ce gwamnatin sa zata taimaka ta haujin samar da kayan aiki domin sojin su kara samun sukunin gudanar da aikinsu yadda ya kamata"
To sai dai an jima mahukunta na cewa za su dauki mataki musamman idan wani ibtila'i ya faru amma kuma a karshe sai maganar ta bi shanun sarki.
Mai magana da yawun gwamnan Sakkwato Abubakar Bawa wanda ya fitar da wata sanarwa bayan kammala taron gaugawa da gwamnan ya gudanar tare da hukumomin tsaro, ya ce "tsarin da gwamnati ta yi ya bambanta da na gwamnatoci da suka gabata, saboda wannan gwamnati tana da azamar ganin an kawar da rashin tsaro.”
“A taron da gwamna ya yi da hukumomin tsaro an gano wasu matsaloli da ke kawo koma baya ga ayukan jami'an tsaro da suka hada da rashin biyan su kudaden alawus har tsawon wata biyar, kuma motocin da suke aiki da su suna cikin mummunan yanayi, ya ce gwamnati ta dauki matakan gyara ga wadannan matsalolin domin daga wannan wata na Yuni za'a ci gaba da biyan kudin alawus ga zaratan jami'an tsaro dake bakin daga suna kula da tsaron al'umma.”
Matsalar rashin tsaro ta jima tana addabar jama'a a Najeriya duk da kokarin da gwamnatocin da suka shude suka ce sun yi na shawo kan ta, yanzu abin jira a gani hubbasar da sabbin gwamnatoci zasu yi da yake wasunsu sun bayar da tabbacin aiki wajen shawo kan matsalolin na rashin tsaro.
Saurari Cikakken Rahoto Daga Muhammadu Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5