Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dokar Hana Almubazzaranci Yayin Bukukuwa A Jihar Sokoto


Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal
Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal

La'akari Da yadda wasu al'adu ko dabi'un al'umma a wasu yankunan Najeriya suke kara kawo matsin a rayuwa musamman ga marasa karfi daga cikin al'umma, gwamnatin jihar Sokoto take kokarin haramta yin almubazzaranci a lokacin bukukuwa.

Mahukunta a Najeriya cikin sauran wa'adin da ya rage musu akan mulki sun ci gaba da yunkurin samar da hanyoyin da za su iya saukaka lamurran rayuwa da kuma kare martabar al'umma musamman marasa karfi .

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da majalisar dokokin jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya ta amince da dokar hana almubazzaranci a lokacin bukukuwa.

Daga cikin al’adun sun hada da wadanda ake samu a lokutan bukukuwa musamman wadanda suka shafi aure, bukin suna da makamantan su a arewacin Najeriya.

Hakan yasa da yawa jama'a na kokawa akan illolin da yin almubazzarancin a lokutan bukukuwan ke haifarwa a cikin al'umma.

Al'ummar jihar Sakkwato ta shiga sahun wasu al'ummomi da suka yunkara don kawo sauyi ga wadannan al'adun ta yadda jama'a zasu rika samun sauki.

Dan majalisar jiha mai wakiltar mazabar Yabo wanda kuma shine shugaban kwamitin lamurran addini a majalisar Abubakar Shamaki Yabo shi ya jagoranci gabatar wa majalisar, wani kudurin doka akan hana almubazzarancin a lokutan bukukuwan.

Dan majalisar yace bisa ga korafe-korafe da suke samu daga jama'a akan illolin almubazzarancin ne yasa dashi da abokin aikin sa dun ga ya dace a sake yin gyara ga dokar ayi ma kwaskwarima ta dace da yanayin da ake ciki yanzu.

Dokar dai ta kayyade abubuwan da za'a rika bayarwa a lokutan neman aure da wasu bukukuwa.

Acewar dan majalisar Sadaki zai kasance kwatankwacin darajar daya bisa hudu na kudin dinari Kamar yadda Musulunci ya amince, kayan neman aure kuwa ba zasu wuce kwandon goro biyu ba, da kwalin alawa biyu da kudi naira dubu ashirin, kayan lefe ma kar wuce turamin atampa goma.

Duk da yake gwamnatin Sakkwato bata kai ga sa hannu ga dokar ba kafin ta soma aiki masana na ganin wannan tsarin zai yi tasiri.

Almubazzaranci a lokutan bukukuwa dai ya jima yana ci wa ‘yan Najeriya tuwo a kwarya, abinda ya kai aka samar da dokokin takaita matsalolin a wasu jihohi kamar kano da Jigawa, har a yankin kudancin Najeriya a wasu jihohi an hada almubazzarancin bukukuwan jana'izar mamata da wasu bukukuwa.

Saurari rahoton Muhammad Nasir:

Hana Almubazaranci.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG