Kasa da sa’o’i 24 da majalisar wakilan tarayyar Najeriya ta ba wa babban bankin kasar wato CBN umarnin dakatar da tsarin adadin tsabar kudi da ‘yan kasar za su rika cira a kowacce rana baya ga koke-koken masu kanana da matsakaitan sana’o’i.
Bankin CBN ya ce ba bu gudu ba ja da baya a game da tsarin da zai fara aiki a ranar 9 ga watan Janairun 2023 mai gabatowa, inda bankin ke cewa ba zai dauki matakin da zai kuntatawa jama’a ba kuma za’a ci gaba da yin nazari don a yi gyare-gyare kan tsarin.
Tun bayan sanarwar da ya fitar a ranar Talata 6 ga watan Disamban, daga babban bankin Najeriya wato CBN na cewa a wani mataki na cimma tsarin hada-hada ba tare da yin amfani da takardun kudi masu yawa ba a bayyane ba wato Cashless Policy a turance ne ‘yan kasar daga sassa daban-daban suka yi ta kokawa a game da yanayin tsaurin tsarin suna mai cewa matakin zai dada jefa al’umma cikin mawuyacin yanayi ne kawai.
Tuni dai ‘yan Najeriyar da suka hada da masu kanana da matsakaitan sana’o’i, kamar masu cire ko saka kudi a asusu na sha’anin POS, masu sayar da wayoyin tarho, da dai sauransu su ka yi ta kokawa tare da nuna fargaba a kan yadda wannan al’amari zai shafi sana’ar su, inda wasu ke cewa hakan zai iya sa su rasa hanyoyinsu na samun abun da zasu rika kaiwa bakin salati.
A wani bangare kuma, masanin tattalin arziki kuma Malami a jami’ar gwamnatin tarayya da ke Kashere a jihar Gombe, Dakta Isa Abdullahi, ya ce duk da cewa gwamnatin kasar na neman cimma tsarin nan na Cashless Policy ne, akwai bukatar ta sake lale a game da lamarin sakamakon yadda ba ta nan gizo ke saka ba kasancewar akwai kauyukka da dama da babu bankuna a cikinsu kuma kadan ne masu harkar POS ma.
Sai dai babban bankin kasar ya ce babu gudu ba ja da baya a game da aiwatar da wannan tsari daga ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2023 kuma zai ci gaba da jin ra’ayoyin al’umma don yin gyara da kuma inganta tsarin.
Daraktan hada hadar kudi Malam Ahmed Bello Umar ya shaida wa VOA cewa Bankin CBN ya yi kira ga ‘yan kasar su kwantar da hankulan su a game da tsarin saboda an yi ne don ci gaban kasa, ba wai don kuntatawa al’umma ba.
A game da shirin bankin CBN na wayar da kan al’ummar kasa dangane da wannan tsarin na rage tsabar kudi da ke yawo a cikin kasar, Malam Ahmed Bello Umar, ya kara da cewa bankin CBN na hada gwiwa da kwamitocin bankunan kasar, hukumar wayar da kan ‘yan Najeriya ta NOA, Sarakunan Gargajiya, Malaman Addini, wakilai na musamman na SINEF, da dai sauransu don fahimtar da al’umma a kan tsarin.
A bangaren kuma sabbin tanade-tanaden babban bankin kasar, majalisar wakilai ta umurci gwamnan bankin CBN ya bayyana a gabanta a ranar Alhamis 15 ga watan Disamba, 2022 domin yi wa majalisar bayani kan dalilan da zasu sanya a yi aiki da sabbin manufofin bankin.
Saurari cikakken rahoton Halima Abdulrauf daga Abuja:
Your browser doesn’t support HTML5