'Yan majalisar dai da ke taruka daban-daban a Abuja; sun ce za su mara baya ga kakaki da sauran shugabannin majalisa ne da za su kare muradun dimokradiyya maimakon na kashin kai.
Sabbin 'yan majalisar daga dukkan jam'iyyu su 243 cikin adadin 'yan majalisa 360 wanda hakan ya nuna har dai za su yi aiki tare to za su iya kawo sauyin da su ke hankoron yi cikin sauki.
Wannan na faruwa ne duk da kasancewar jam'iyyar APC mafi rinjaye ta fidda sunayen wadanda ta ke so su zama shugabannin majalisar dattawa da wakilai.
Sabon dan majalisar wakilan daga Sokoto Bashir Usman Gorau ya ce sun yanke hukuncin aiki tare ba tare da nuna bambancin siyasa ba.
Masana kimiyyar siyasa na nuna za a iya samun bambanci tsakanin takun shugaba Buhari da zabebben shugaba Tinubu ga zaben shugabannin majalisar in a ka tuno majalisar dattawa ta 8 inda Bukola Saraki ya zama shugaba ba tare da amincewar jam'iyya ko shugaban ba; kuma Ike Ekwremadu daga PDP ya zama mataimaki.
Dr. Farouk BB Farouk masanin siyasa ne a jami'ar Abuja da ke cewa in 'yan majalisar sun jajirce za su iya kaucewa zama 'yan amshin shatan fadar Aso Rock.
Dan APC na bangaren shugaba Buhari Magaji Muhammad Yaya ya ja hankalin 'yan majalisar da hada kai don kare hadin kan kasa fiye da muradun siyasa.
Majalisar dokokin dai ta 10 za ta fara aiki a watan gobe bayan rantsar da sabuwar gwamnati a karshen watan nan.
Saurari rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5