Ita ma gwamnati a na ta bangare ta dauki alkawalin share hawayen masu aikin sufuri a game da wasu matsalolin dake haddasa cikas ga sha'anin sufurin, matakin da masu kare hakkin mabukata suka sha alwashin bin sa sau da kafa don ganin bangarorin sun cika alkawali.
Tun a washegarin bayyanar matakin karin kudin man gazoil din da gwamnatin Nijer ta dauka a bisa dalilan da ta danganta da yakin Rasha a Ukraine, ministan sufuri da minstan kasuwanci da na man fetur da na makamashi da na kudin kasa suka shiga tantaunawa da shugabanin kungiyoyin masu motocin jigilar fasinja da na dakon kaya don zakulo hanyoyin takaita matsalolin da ka iya biyo bayan wannan mataki, abin da ya bada damar cimma matsaya.
Su ma masu motocin jigila wadanda suka hada da na tashoshin kananan motoci da na kamfanonin jigilar fasinja da masu motocin dakon kaya sun amince ba zasu kara kudin mota ba kamar yadda babban darektan kamfanin Al ‘izza transport Mohamed Albakaye, ya bayyana.
Kungiyoyin kare hakkin mabukata sun sha alwashin bin diddigin wannan yarjejeniya don ganin bangarorin ba su saba alkawali ba inji shugaban kungiyar ADDC WADATA Malan Maman Nouri.
A nan gaba gwamnatin ta ce za ta fara irin wannan tattaunawa da kungiyoyin drebobin taxi domin cimma yarjejeniya a kan maganar kudin motocin haya a biranen kasar.
Matakin karin kudin man diesel wani abu ne da hukumomin Nijer suka ce sun bullo da shi domin takaita yawan motocin dake shigowa kasar daga waje don sayen man da araha lamarin da suka ce idan ba a yi wani abu akai ba zai iya shafar ayyukan tsaron kasa.
Saurari rahoton Souley Moumouni Barma cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5