Ba Za A YI Hawan Sallah A Kano Ba Bana

Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero (C), lokacin cika shekaru 50 da hawa karagar mulki

Majalisar masarautar Kano tace a bana babu haye-hayen dawaki da aka saba yi na al’ada yayin bukukuwan sallah sanadiyyar balaguron da mai martaba sarki Alhaji Ado Bayero yayi.
Majalisar masarautar Kano tace a bana babu haye-hayen dawaki da aka saba yi na al’ada yayin bukukuwan sallah sanadiyyar balaguron da mai martaba sarki Alhaji Ado Bayero yayi zuwa kasashen ketare.

A wata sanarwa da masarautar sarkin Kano ta bayar ta bakin babban dan majalisar sarki, wamban Kano Alhaji Abbas Sanusi, ta umurci hakimai a duk kananan hukumomi 44 na jihar Kano su zauna a garuruwansu su yi sallah tare da gudanar da hawan dawaki a yankunansu.

Domin haka a maimakon jawabin da mai martaba sarki yake gabatarwa, yayin hawan sallah a kofar kwaru bayan dawowa daga masallacin Idi, a wannan karon wamban Kanon ne zai gabatar da sakon sallah ga jama’a a zauren majalisar Sarki dake kofar kudu, haka nan kuma ranar biyu ga Sallah, a maimakon hawan nasarawa, Wamban Kano zai jagoranci hakimai zuwa gidan gwamnati domin gaisawa da gwamna. A cikin hirarsu da wakilin Sashen Hausa Mahmud Ibrahim Kwari, Kanawa sun bayyana yadda suka ji dangane da wannan sanarwar.

Your browser doesn’t support HTML5

Babu hawan durba bana a birnin Kano - 1:30