Ba Yau Aka Fara Sauka Da Tsani Daga Jirgin Sama Ba a Najeriya

Wani Jirgin Fasinjan Kamfanin Aero a Najeriya

A makon da ya gabata ne sai ga wani faifan bidiyo a shafukan abota na internet yana ta yawo kamar wutar dare. Inda aka ga wasu mutane suna sauka ta tsanin hawa katanga daga wani katafaren jirgin fasinjar kamfanin Aero a Bauchi, Najeriya.

Ba kamar yadda aka saba ganin wata mota ta sulala dauke da katafariyar matattakalar bene har zuwa inda jirgi ke tsaye a filin saukarsa ba. Maimako haka sai gashi ana a tara atara da dogon tsani. Aka kuma kanga shi a jikin kofar jirgin inda jama’a suka dinga sauka a tsorace.

Wannan abu y agama gari inda har maganar ta kai kunnen hukumomin da abin ya shafa na sufurin jiragen sama. A karshe dai Ministan harkokin safarar jiragen sama Hadi Sirika ya bada umarnin a binciki lamarin da suke ganin abin kunya ne a kasa kamar Najeriya.

To sai dai wani tsohon direban jirgin sama Kaftin Bala ya bayyana cewa wannan ba karon farko da irin haka ke faruwa a kasar ba. Domin kuwa ya tuna lokacin da aka yi irin wannan saukar ta matakalar tsani maimakon ta jirgin sama.

Sai dai ya bayyana dalilan da yasa hakan ta kan faru, amma ya bada shawarar yadda ya kamata gwamnatocin jihohi su yi don gujewa wannan abin kunyar da ya faru a filin saukar jiragen saman jihar Bauchi a Najeriya.

Your browser doesn’t support HTML5

Ba Yau Aka Fara Sauka Da Tsani Daga Jirgin Sama Ba a Najeriya - 4'12"