A 'yan shekarun nan gwamnatocin jihohin Najeriya sun yi rubdugun kai wasu daliban jihohinsu zuwa karo ilimi a kasashen duniya bisa matakai daban-daban, a tsarin da suke ganin wata sila ce ta ciyar da al'ummar jihohinsu gaba bayan sun dawo. to amma yawanci daliban na ta kokawa da cewa ba a kula da su.
Daliban Najeriya da dama da ke karatu a kasashen waje bisa tallafin karatun gwamnati suna kokawa da cewa an kaisu an baro ba tare da ci gaba da kula da su yadda ya kamata ba.
Sai dai kuma wasu jami’an gwamnati yawanci suka musanta cewa daliban na shan wuyar da cewa wani lokaci kamar zuzutawa suke yi. Wakilinmu Murtala Faruk Sanyinna ya tuntubi daya daga jami’an gwamnati akan lamarin.
Inda ya nuna cewa har da gajen hakuri, domin kuwa ma wasu an biya musu kudaden shekaru daya zuwa biyu na zangon karatun da aka tura su yowa a kasashen.