Ba Sanya Wa'adin Daina Amfani Da Tsaffin Takardun Naira Ba - CBN

Babban bankin Najeriya CBN

Kotun kolin ta ba da umarnin cewa za a ci gaba da karbar takardun kudin na naira 200 da 500 da 1000 tare da sabbin da aka sauyawa fasali.

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya musanta rahotanni dake cewa za'a daina karbar tsaffin takardun kudi na naira 200 da 500 da 1000 daga ranar 31 ga watan Disemba mai zuwa.

A sanarwar da daraktar yada labaransa, Hakama Sidi ta fitar a jiya Alhamis, CBN yace za'a cigaba da amfani da umarnin da kotun kolin Najeriya ta bayar a Larabar da ta gabata, 29 ga watan Oktoban bara har sai illa masha-allahu.

"Muna so mu bayyana karara cewa babu kamshin gaskiya game da wadannan rahotanni kuma ana yada su ne da nufin kawo cikas ga tsarin hada-hadar kudin Najeriya.

"Domin gusar da shakku, ina mai jaddada cewa umarnin Kotun Kolin Najeriya na 29 ga watan Oktoban bara, wanda ya amsa bukatar antoni janar na tarayya kuma ministan shari'a ta tsawaita wa'adin amfani da tsaffin takardun kudin har sai illa masha-allahu, na nan daram.

Kotun kolin ta ba da umarnin cewa za a cigaba da karbar takardun kudin na naira 200 da 500 da 1000 tare da sabbin da aka sauyawa fasali.