Ba Mu Goyi Bayan Yin Sulhu Da ‘Yanbindiga A Jihar Neja Ba - Masanin Tsaro

Yan bindiga a jihar Neja

Masana harkokin tsaro a Nijeriya na ci gaba da nuna shakku akan matsayin da gwamnan Jihar Neja ya dauka na cewa yana son yin sulhu da ‘yan bindiga da ke ci gaba da hallaka jama’a a jihar.

Gwamnan jihar Nejan Umar Muhammed Bago dai ya fito fili ya nuna bukatarsa na ganin an yi sulhu da wadannan ‘yan bindiga da ko a cikin makon jiya sun hallaka sojojin Nijeriya kimanin 30 a jihar tare da kwashe dubban shanun mutane daga yankin Zungeru.

A yanzu dai rahotanni sun tabbatar da cewa mayakan kungiyar Boko Haram sun sake kafa tutarsu a yankin Shiroro dab da daya daga cikin madatsun ruwan da ke samar da hasken lantarki a Nijeriya.

A hirarsa da muryar Amurka, Hon. Suleman Dauda Chukuba tsohon sojan Nijeriya kuma tsohon shugaban karamar hukumar Shiroro mai fama da wadannan ‘yan bindiga, ya ce ba ya goyon bayan yin sulhu da wadannan mahara, domin ko a baya ma an yi hakan amma ba a samu nasara ba.

Ya kara da cewa, sun saba karbar miliyoyin kudi na kudin fansa, don haka bai ga abin da za a yi masu su daina ba.

Suleman Chukuba yace ko sauran jihohin da a ka ce an yi sulhun kamar jihar Zamfara, lamarin bai yi tasiri ba.

A yanzu dai ko baya ga batun yin sulhun, gwamnatin jihar Neja tace zata kara janyo Sarakuna iyayen kasa cikin lamarin domin samun nasara, a cewar sabon kwamishinan kananan hukumomi da Masarautu na jihar Nejan, Alh.Mu’azu Hamidu Jantabo.

Saurari cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Bamu Goyi Bayan Yin Sulhu Da ‘Yanbindiga A Jihar Nejan Nigeria Ba - Masanin Tsaro