Na fuskanci kalubale da dama daga wajen al’umma mussamam ma ganin cewa a harkar waka na zabi fannin hip-hop, a maimakon wakar nanayen ko ta soyayya da mata suka saba rerawa inji mawakiya Zainab Ishak Mahmoud, waccce aka fi sai da Queenzeeshark.
Matashiyar ta bayyana hakan ne yayin zantawarsu da wakiliyar DandalinVOA a Kanon Najeriya, wacce ta ce ta tsunduma harkar wakar gambara wato hip-hop domin ta nunawa al’umma cewar wakokin hip-hop ba’a alakarta su ga maza kadai ba .
Ta kuma kara da cewa burinta dukkanin sakonnin da take fitarwa su kasance masu amfanar da al’umma, tare da bukatar mutane su nuna mata gyara a wauraren da suka ga akwai bukatuwar hakan.
Mutane da dama sun kalubalance ta akan dalilan da suka sa ta shiga harkar hip-hop, amma da ta juri cecekucen ta cimma burinta har ma a cewar ta, lamarin ya kai ga mutane na jiran duk wata sabuwar waka da zata fitar tare da yawaita tambayarta ko yaushe sabuwar wakarta zata fito domin nuna karbuwarsu da son sauraren wakokinta.
Your browser doesn’t support HTML5