Sharar wasu jari ce ga wasu mutane, dagwalon da kamfanonin dake nika gyada domin fitar da man gyada shine mafi akasarin mata da ke yankin Dawakin Dakata masu sana’ar dogaro da kai ke amfani dashi wajan kula da kansu da yayansu in ji Zainab Abdullahi.
Tace suna sana’ar man laka ne wato , dagwalon da ake fitar wa bayan an nika gyada aka kuma fitar da mai girki ragowar ruwan da ke tattare da harkar matse man gyada wanda ba shi da amfani ga kamfanin shine suke kara sarrafawa domin fitar da man girki da abincin kaji.
Zainab Abdullahi ta bayyana wa wakiliyar dandalinVOA Baraka Bashir, cewa mafi akasarin matan dake yankin Dawakin Dakata karamar hukumar Nassarawa dake kanon Nijeriya, da wannan sana’ar ne suka dogara.
Mal Abubakar Baba Salau shugaba kuma mai bada dagwalon man gyada a Dawakin dakata ya bayyyana cewa mafi yawan mata nan na sayan ragowar dagwalon da suka fitar na man gyada wanda da shi ne suke samar da man gyadan da kuli-kulin da ake bawa kaji sai dosan da ake saffara sabulun soda da shi.
Wani babban dila Mal. Mohammad Saminu da ake matse masa man gyada a kanfanin ya yi bayani ya ce dagwalon man gyada na taimakawa wadanda mata wajen harkokinsu na yau da kulum.
Su dai wadanda mata sun ce wannan sana’ar da ita suka dogara kuma tana taimaka masu wajan biyan bukatunsu da na ‘ya’yansu.