Cikin 'yan-kwanakin nan dai labarin sakin Sadiq Ango Abdullahin daya daga cikin mutanen da 'yan-bindiga su ka sace a jirgin kasan da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ya cika kafafen sada zumunta, sai dai kuma gamayyar iyalan wadanda aka sacen tace har yanzu ba a saki Sadiq Ango Abdullahin ba, kamar dai yadda wasu daga cikin su su ka tabbatar.
A maimakon shagulgulan Sallah da al'umar Musulmi ke sha yanzu haka, 'yan'uwan mutanen da aka sacen sun ce su kunci su ke ciki.
Sai dai a jawabi shugaban Kasa Muhammadu Buhari na ranar Sallah ya bada wani tabbachi.
Shugaba Buhari ya ce ya baiwa rundunonin tsaro umarni su tabbatar da ceto dukkan wadanda aka sace cikin gaggawa kuma lafiya lakau, ya kuma ce ya umarci hukumar jiragen kasa ta bude wata cibiyar bibiyar yadda za a ceto dukkan mutanen da ke hannun 'yan-bindiga sannan su rinka bada bayani akai-akai ga iyalan wadanda aka sacen. Shugaba Buhari ya ce wannan zai rage musu radadi da damuwa, a yayin da gwamnati ke cigaba da kokarin ceto wadannan aka sace don sada su da iyalan su.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5