Babu Gaskiya A Jita-jitar Rushe Masallacin Abuja - Hukumar Raya Abuja

Babban Masallacin Abuja

Hukumar raya Babban Birnin Tarayya na Abuja ta ce sam ba kamshin gaskiya a labarin da aka yi ta yayata a kafafen sada zumunta cewa Ministan birnin Nyesom Wike zai rushe wani sashen babban Masallacin tarayya da ke Abuja.

ABUJA, NIGERIA - Babban sakataren hukumar FCDA a takaice Injiniya Shehu Hadi Ahmed, ya ce ba abin da zai shafi jikin Masallacin.

Engineer Shehu Hadi Ahmad

Babban Masallacin Abuja wanda ke tsakiyar birnin na zama bigiren da matukar mutum ya shigo Abuja zai ga hasumiyarsa daga nesa kuma shi ne mafi girman Masallaci inda a ke yi wa kasa addu'ar salama musamman lokacin azumin watan Ramadan.

Shehu Hadi ya ce aikin fadada hanya zai ratsa ta daya daga filaye mallakar masallacin da ke gefe wanda wani kwari ko kwazazzabo ya raba shi da masallacin “Kwamitin masallacin tun farko ya nemi filin ne ba don fadada Masallacin ba amma don gina shaguna ne da wasu abubuwa makamantan hakan.”

Imam Kabir Adam

Ga tunanin ko ministan Abuja Wike na da wata mummunar manufa kan masallacin; Injiniya Hadi ya ce duk maganar da mutum zai yi ya yi bincike tukun kafin yanke hukunci.

“Mun kai wa minista ya amince a ba wa Masallacin filin da zai rage bayan hanyar kuma a musanyawa Masallacin wani fili don yin aikin da ya yi niyya.”

Shugaban kwamitin kula da Masallacin Etsu Nupe da tawaga sun gana da hukumar ta Abuja inda suka cimma matsaya da ta kara zayyana Masallacin da babbar Majami'ar da ke yankin da wasu alamu masu daraja na kasa da ake tunkaho da su.

Saurari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-Hikaya:

Your browser doesn’t support HTML5

Babu Gaskiya A Jita-Jihar Rushe Masallacin Abuja - Hukumar Raya Abuja