Ba Dole Ba Ne Amurka Ta Cigaba da Amincewa Taiwan Bangaren China Ce - Trump

Shugaban Amurka Donald Trump mai jiran gado

Jiya shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump yace shi bai ga dalilin da Amurka zata cigaba da mincewa da kasar Tawan a matsayin bangaren kasar China ba.

Idan har Amurka zata cigaba da daukar Taiwan a matsayin bangaren China to dole ne ita Chinar ta shafawa Amurka romo a baka kamar ba Amurka fifiko da sassauci a harkokin kasuwanci.

A wata muhawara da yayi a gidan talibijan din Fox Donald Trump baya son China ta dinga fada masa abun da zai yi ko ya kamata yayi.

Ya kare amsa kiran da shugaban Taiwan Tsai Ing-wen yayi masa ta wayar tarho. Irin wannan kiran shi ne na farko tun shekarar 1979 lokacin da Amurka ta amince Taiwan bangaren China ce.

Donald Trump yace babu wani dalilin da Amurka zata amince da Taiwan a matsayin bangaren China, saidai idan China ta bada kai bori ya hau a harkokin kasuwanci.

Shugaban mai jiran gado ya zargi China kan manufofin takardar kudinta da yadda take tara dakarun soji a kudancin tekun China da kuma yadda ta gaza hana makwafciyarta Koriya ta Arewa cigaba da gwajin makamai masu linzami.

A halin yanzu China tana karbar harajin kaso 9.7 cikin dari kan kayan da suka shiga kasar daga Amurka yayinda ita Amurka ke karbar kaso 2.9 kacal cikin dari akan kayan China da suke shiga kasar.

Tun can farko China ta zargi Donald Trump da amsa kira daga shugaban Taiwan abun da Trump yace da bai amsa kiran ba zai zama rashin da’a ga wanda ya kirashi ya tayashi murnar zabensa.