Captain Aden Hassan, yace fashewar ta auku ne a gaban shagon sayar da abinci, wanda ke kusa da gidan tsohon jakadar Turkiyya, dake yankin Hodan.
Hassan yace anji wannan karar kusan duk a fadin birnin, sai dai kawo yanzyu basu san irin adadin barnar da wannan fashewar ta haifar ba.
Shima Abdifatah Halane, wanda shine mai Magana da yawun gundumar da abin ya faru ya jaddada wannan batu, yace an shaida masa cewa mutun daya ne ya samu rauni.
Halane, yace jami’an tsaron da suka bamu wannan bayanin sun tabbatar mana cewa mutun guda ne abin ya shafa , kuma munyi imanin cewa ba kowa ne ya aikata wannan abu ba illa Al-shabab.
Kawo yanzu dai ba cikakken bayanin wannan al’amari domin ko ababen hawa da zirga-zirgar mutane kan takaita ne a birnin da zarar karfe 8 na dare yayi.
Wannan fashewar ta biyo bayan wadda ta faru ne da rana, kuma ta yi dalilin mutuwar mutane 7 kana mutane 15 suka samu rauni