Karancin Maganin Kashe Dafin Maciji A Najeriya

Karancin maganin kashe dafin maciji a Najeriya ya kasance babban kalubale da yasa ake samun yawaitar mutuwar mutanen da maciji ya sare su a sassa daban daban na kasar.

Jihohin dake da matsalar saran maciji a Najeriya sun hada da Plateau, Nasarawa,Benue Gombe, Bauchi, Adamawa da Taraba.

Shugaban asibitin dake kula da sarar maciji, wani sashe na asibitin jami’ar Jos, dake garin Zamko dake karamar hukumar Lantang ta kudu, a jihar Plateau, Dr. Titus Dajel, yace matsalar da ake fuskanta wajen jinyar shine karancin maganin sarar macijin, da yanzu haka aka dena shigo dashi daga kasar wajen.

Yana mai cewa Zamko, na yankin Langtang, akan samu mutane kama daga dari zuwa dari da hamsin dake zuwa asibiti dalilin sarar maciji a kowane wata, amma a kwanaki nan da yake babu magani da yawa daga cikinsu kan mutu a wata Oktoba kawai an samun mutane goma da suka mutu saboda rashin maganin sarar maciji.

Dr.Titus Dajel, ya bukaci gwamnati da ta dauki matakan ganin cewa an fara samarda maganin sarar maciji a Najeriya, batare da bata lokaci ba ganin cewa tun lokaci shugaba Obasanjo, ne ya bada umarni cewa a gina wurin da za a fara sarrafa maganin sarar maciji.

Your browser doesn’t support HTML5

Ba a Samarda Maganin Sarar Maciji A Najeriya - 5'00"