Shugaban Kwamitin Kungiyar ba da agaji ta Red Cross Peter Maurer, ya kai ziyarar aiki a kasar Kamaru inda ya tattauna da hukumomin kasar kan ‘yan gudun hijra da ke gujewa rikicin Boko Haram daga kan iyakokin kasar.
Har ila yau Mr Maurer ya tattauna da Firai ministan Kamaru Philemon Yang, kan batun masu yin kaura da rikicin na Boko Haram bai shafa ba.
A kididdigan da kwamitin na Red Cross ya bayar, ya nuna cewa yankin Tafkin Chadi na dauke da ‘yan gudun hijra sama da miliyan daya kuma mafi yawansu suna cikin kasar Kamaru ne.
A cewar Mr Maurer, ya kai ziyarar ne domin kuma ya mika godiyarsa ga gwamnatin Kamaru kan irin taimakon da ta ke baiwa ‘yan gudun hijrar, kana ya ce kungiyar ta Red Cross na so ta fadada ayyukanta a cikin kasar ta Kamaru.
“Kwamitin na Red Cross da hukumomin Kamaru suna duba yadda za su fadada irin taimakon da suke kawowa masu bukata kamar abubuwan da suka shafi sama musu shimfida da abinci da kuma kiwon lafiya” In ji Maurer.
Mr Maurer ya kara da cewa baya ga ba da agaji ga masu bukata, kungiyar ta Red Cross na taimakawa wajen hada iyalan da yaki ya raba su.
Kungiyar ta Boko Haram ta samo asali ne daga arewa maso gabashin Najeriya inda ta yi sanadiyar mutuwar dubban mutane kana ta raba wasu miliyoyi da muhallansu.
Your browser doesn’t support HTML5