Kimanin ‘yan Najeriya 300, ne aka dawo dasu gida daga kasar Libya a wani shirin maida bakin haure kasashen su. ‘Yan Najeriyan dai sun kan hanyarsu ta zuwa kasashen turai ne domin samu rayuwa da kuma kaucewa fadace fadace.
Sun dai ‘yan Najeriyan dari biyu da hamshin da takwas an dawo da sune a cikin wani jirgin kasar Libya, ta babban filin jirgin sama na kasa da kasa na Murtala Muhammad dake Lagos.
A jawaban da suka gabatar ga ‘yan gudun hijirar da aka dawo dasu gida daga kasar Libya wace yaki ya daidaita jami’an NEMA suyi kira ga wadanda aka dawo dasu su kwantar da hankulansu su koma kan ayukan su da suka bari a gida Najeriya, domin cire da kasar gaba kuma su sani cewa babu wata kasa da ta fi Najeriya watau kasar su ta asali.
Babban jami’an hukumar NEMA, mai kula da kudu maso yammacin Najeriya, Dr. Bamidele, yace ‘yan kudun hijiran da aka dawo dasu maza sunfi yawa kuma ya kara da cewa kamar yadda aka sani jihohin Edo da Delta sun fi yawan mutanen da akae dawowa dasu daga kasashen ketare masammam kasar ta Libya.
Hukumar kula da ‘yan kudun hijira na kasa da kasa tare kuma da hadin guiwar kasar Libya da Najeriya ne suka hannu domin dawo da wadannan ‘yan Najeriyan zuwa gida.
Rahotanin ya nuna cewa ‘yan Najeriyan ne suka bukaci da a maido dasu gida domin kashin kansu sakamakon wahalhalu da dama da suke fuskanta a kasar ta Libya.
Your browser doesn’t support HTML5