Auren Funke Akindele Da JJC Skillz Ya Mutu

Abdulrasheed Bello (JJC Skillz) da Funke Akindele (Hoto: Instagram/Funke Akindele/PhotoKulture)

Abdulrasheed Bello (JJC Skillz) da Funke Akindele (Hoto: Instagram/Funke Akindele/PhotoKulture)

“Na san cewa, na yi iya bakin kokarina wajen ganin abubuwa sun daidaita, amma daga karshe na gane cewa, al'amura sun riga sun rincabe.” In ji Bello.

Mawaki Abdulrasheed Bello wanda aka fi sani da JJC Skillz ya sanar da mutuwar aurensu da fitacciyar jarumar Nollywood a kudancin Najeriya Funke Akindele.

Bello ya bayyana hakan ne a shafinsa na Instagram da safiyar ranar Alhamis, inda ya ce sun kwashe tsawon shekara biyu auren nasu na fuskantar matsaloli.

“Ya ku abokanai da ‘yan uwa, Ina so na sanar da ku cewa ni da Funke mun rabu. A lokacin zaman auren namu, mun yi abubuwa da yawa tare, mun samu kyawawan yara biyu. Sai dai shekaru biyun da suka gabata, sun kasance masu sarkakiya a gare mu.

“Na san cewa, na yi iya bakin kokarina wajen ganin abubuwa sun daidaita, amma daga karshe na gane cewa, lamurran sun riga sun rincabe.” In ji Bello.

Wata takaddama da auku tsakanin ma’auratan biyu a farkon shekarar nan, ta kai ga Funke ta kori Bello daga gidanta, lamarin da Bello ya tabbatar a sakon da ya wallafa.

“Watanni uku da suka gabata, Funke ta nemi na fita mata daga gida, ban da haduwar da muka yi a wajen bikin karrama jarumai na AMVCA, na yi ta kokarin na ga mun zauna da Funke mun sasanta al’amuranmu, amma abin ya ci tura.

“Na fito na yi wannan sanarwar ce, saboda jama’a sun san cewa kowa ya yi hanyarsa, ko da yake, akwai batutuwa da suka rage tsakaninmu, kamar wanda zai rike yara, wanda batu ne mai muhimmanci da kuma harkokin kasuwancinmu da muke yi tare, amma na san cewa za a warware komai cikin lumana.”In ji JJC Skillz.

Sai dai mawakin ya rufe sashen yin tsokaci a sanarwar da ya wallafa a Instagram, wanda hakan ba zai ba mutane damar tofa albarkacin bakinsu kan lamarin ba.

Sai dai duk da matsalolin da suke fuskanta, a ranar 19 ga watan Yunin nan, Funke ta wallafa wani bidiyon Bello a shafinta na Instagram yana rawa, inda take taya shi murnar ranar mahaifi da aka yi.

A shekarar 2016 Bello da Funke suka yi aure, sun kuma haifi yara ‘yan biyu a 2018.