Attajirai Hudu Mafiya Arziki A Najeriya

Fobes

Mujallar Fobes ta fitar da jerin sunayen hamshakun attajirai a duniya da su ka fi kudi na shekara ta 2024 da su ka hada da ‘yan Najeriya.

Bisa ga jerin sunayen da mujallar ta fitar, Alhaji Aliko Dangwate har yanzu yana kan gaba a matsayin mutumin da ya fi kowa kudi a Najeriya,

Banda Dangwate, mujallar ta bayyana Abdul Samad Rabiu mai kamfanin BUA a matsayin attajiri na biyu da ya fi kudi a Najeriya. Sai Mike Adenuga, wanda ya kafa Globacom, a matsayin mafi arziki na uku a Najeriya, sai Femi Otedola wanda ya ke da jari a bangaren mai da iskar gas, da bangaren wutar lantarki da kuma harkokin banki.

Mujallar Fobes ta bayyana Elon Musk a matsayin wanda ya fi kowa kudi a duniya, wanda ya mallaki $3.7 B. Larry Ellison yana matsayi na biyu da $3.6 B . Sai kuma Jeff Bezos a matsayi na uku da $2.7 B . Sai matashi dan shekaru 40, Mark Zuckerberg a matsayin mutum na hudu. mafi arziki a duniya.