Wani kakakin kasar ta Korea ta Arewa a ma’aikatar harkokin wajen kasar, ya fada a wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ta kafar kamfanin dillancin labaran kasar na KCNA, tambayar yanzu ita ce, “yaushe ne ainihin yakin zai barke.”
Ya kara da cewa “mu bama fatan barkewar yaki, amma idan ya zo, ba za mu guje mai ba.”
Korea ta Arewan ta fitar da wannan sanarwar ce, bayan da wani jirgin saman yakin Amurka mai suna B- 1B mai lugudan wuta, ya ratsa ta sararin samaniyar Korea ta Kudu, a wani mataki na sa ido kan abinda ke faruwa, yayin da suke gudanar da atisayen hadin gwiwa da ya tattaro daruruwan jiragen yaki na sama, ciki har da jiragen yakin zamani na Stealth Fighter Jets da Amurka take tunkaho da su.
Wannan atisayen dai na zuwa ne bayan da Korea ta Arewa ta yi gwajin makami mai linzami mai karfin gaske, kuma zai iya ratsa nahiyoyi, wanda kwararru suka ce zai iya kai wa ga Amurka.