Atiku Ya Sa Hannu a Yarjejeniyar Zaman Lafiya, Ya Kalubalanci Buhari

Dan takarar shugaban Najeriya, Atiku Abubakar

Rahotanni sun ce bayan da Atiku ya rattaba hannu a yarjejeniyar, ya yabawa shugaba Buhari saboda sanya hannu da ya yi a yarjejeniyar. Amma ya kalubalance shi da ya sa hannu a kudurin dokar zaben da aka yi wa garanbawul wacce majalisar dokokin kasar ta gabatar masa.

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP a Najeriya, Atiku Abubakar ya rattaba hannu a yajejeniyar tabbatar da zaman lafiya a zaben 2019 da ke tafe.

Atiku ya sanya hannu a yarjejeniyar ce a yau Laraba a cibiyar Kukah da ke birnin Abuja, bayan da ya gaza halartar taron a jiya Talata.

Dan takarar na jam'iyyar PDP mai adawa, ya yi ikrarin ba a gayyace shi zuwa taron ba.

Amma kwamitin da ya shirya taron, wanda tsohon shugaban Najeriya na mulki soja, Abdulsalam Abubakar ke jagoranta, ya ce ya aikawa da kwamitin yakin neman zaben Atiku wasikar gayyata

Rahotanni sun ce bayan da Atiku ya rattaba hannu a yarjejeniyar, ya yabawa shugaba Buhari na jam'iyyar APC saboda sanya hannu da ya yi a yarjejeniyar.

Amma ya kalubalance shi da ya sa hannu a kudurin dokar zaben da aka yi wa garanbawul wacce majalisar dokokin kasar ta gabatar masa.

Wannan yarjejeniya wani shiri ne na ganin an gudanar da zaben na 2019 cikin lumana.

A shekarar 2015, shugaba Buhari, a lokacin yana dan takara da tsohon shugaba Goodluck Jonathan, sun sanya hannu a irin wannan yarjejeniya.