Jerin sunayen kasashen da ke fama da ta’addanci na shekarar 2018, ya nuna cewar Najeriya ce kasa ta uku da ta fi fama da matsalar hare-haren ta’addanci a Duniya.
Rahoton hukumar da ke kididdiga kan ayyukan ta’addanci ta ce, Najeriya kan fuskanci wannan matsalar ce sanadiyar hare-haren ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram, da kuma rikice-rikicen makiyaya da manoma, kamar yadda jaridar yanar gizo ta Premium Times ta wallafa.
Tun bayan rahoton shekarar 2014 da ya ayyana Najeriya a mataki na hudu, Najeriya tana cikin matsanancin hali da ya barta a mataki na uku, a cewar hukumar da ke kididdiga ta Global Terrorism Index (GTI).
Rahoto wanda aka fitar a ranar Laraba, ya saka Iraqi da ke gabas ta tsakiya, a matsayin kasa ta farko, matakin da take kai tun daga shekrar 2014.
Sai kasar Afghanistan ita ke biye mata a matsayin kasa ta biyu.
Kasar Syria ita ce kasa ta hudu, sannan kasar Pakistan ita ce kasa ta biyar a cikin kasashen da suka fi yawan ta’addanci.
Daga cikin ragowar kasashe 10 da suka fi yawan hare-haren ‘yan ta’adda tun daga shekarar 2017, sun hada da kasar Somalia a mataki na shida, sai kasar Yemen a mataki na bakwai, kana Masar a mataki na tara, sannan ta goma ita ce kasar Philippines.
Abun ban sha’awa shi ne, an samu raguwar yawaitar mace-mace a sanadiyyar hare-haren ‘yan ta’adda a Najeriya a shekarar 2017, kamar sauran shekaru da suka bagata a cewar rahoton.
Facebook Forum