Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP a Najeriya a zaben 2023, Atiku Abubakar, zai gudanar da taron manema labarai a ranar Litinin.
Wata sanarwa da jam’iyyar ta PDP ta wallafa a shafukan sada zumunta ta ce Atiku zai yi magana kan wasu muhimman batutuwa da suka shafi kasa.
“Dan takarar shugaban kasa karkashin gagarumar jam’iyyarmu ta PDP a zaben Fabrairu 25 na shekarar 2023 kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, Wazirin Adamawa, zai yi wani muhimmin taro na manema labarai.
“Zai tabo muhimman batutuwa da suka shafi kasa.” Sanarwar wacce ke dauke da sa hannun Sakataren yada labaran jam’iyyar ta PDP ta ce.
Wannan zai zamanto karo na farko da Atiku zai yi magana tun bayan da kotun koli ta kori karar da ya daukaka a kotun don kalubalantar nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A ranar Alhamis kotun koli ta kori karar Atiku da ta Peter Obi na Labour Party inda ta jaddada nasarar Tinubu a zaben na 2023.