A shirnmu na mata DandalinVOA ya samu bakoncin matashiya Asma’u Halilu Abdulkadir, yar asalin jihar Kano wacce ta yi dukkannin karatunta a Kanon Dabo.
Asma'u ta ce tun daga makarantar firamare har sakandare a jihar Kano ta yi, ta kara da cewar kwas din da ta nema ba shi ta samu ba a jami’a. Dalilin haka sai ta karanci Biochemistry wato ilimin hade-haden magunguna.
Asma’u ta ce kamar sauran dalibai ta fuskanci matsala ta malamai, amma matsalar ta zo mata da sauki domin bai kawo mata cikas ba a harkar karatunta.
Ta kara da cewa ko da ta tsinci kanta da rashin samun abinda ta ke so, hakan bai sa ta yi kasa a gwiwa ba, sai dai ma ya kara mata hazaka da jajircewa wajen kammala karatunta cikin sauki.
Ta ce da ta samu matsala da malami wanda yake duba mata aikin ta na kammala karatu, sai da ta kai ga hukumomin makaranta, wanda daga baya aka warware matsalar.
Wajen yi wa kasa hidima, ta ce bata fuskanci matsala ba kamar sauran dalibai, ta yi shi cikin sauki, kasancewar inda aka tura ta yayi dai-dai da karatun da ta karanta.
A saurari cikakken rahoton daga wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir.
Your browser doesn’t support HTML5