Rahotanni na nuna cewa wasu mayakan Asbinawa magoya bayan gwamnati, sun kwace iko da birnin Kidal na arewacin Mali, bayan da fada ya barke tsakanin mayakan da wata gamayyar 'yan tawayen Asbinawa.
WASHINGTON D.C —
Wani ganau ya gaya ma Sashin Faransanci na Muryar Amurka cewa zuwa daren jiya Alhamis, mayakan na Gatia na kakkabe garin don kau da duk wani gyauron 'yan tawaye da watakila su ka boye. To amma har yanzu ana cikin halin rudami a Kidal, kuma ba a tantance ko akwai wadanda abin ya rutsa da su ba.
Ambeyri Ag Rissa, shugaban gamayyar Asbinawa -- mai tasiri a kungiyar Azawad -- ya ce yanzunnan jami'ai su ka kammala ganawa kan wata yarjajjeniya, wadda aka cimma ranar Lahadi kan yadda za a raba iko da birnin, bayan da aka barke da musayar wuta.
Ko lokacin da ya ke maganar, ana iya jin karar bindigogi masu sarrafa kansu.