Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Wakilin Vatican Ya Yi Kira Ga Shugaban Sudan Ta Kudu


Wani babban wakilin Vatican ya yi kira ga Shugaban Sudan Ta Kudu Salva Kiir da Mataimakin Shugaban kasa na daya Riek Machar da su kawo karshen tashe-tashen hankulan da su ka dabaibaye Jabu babban birnin kasar.

Rikicin ya dauki lokaci har na tsawon kwanaki hudu a makon jiya, wanda ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane ya kuma raba dubbai da muhallansu.

Cardinal Peter Kodwo Turkson ya gana da Kiir Jiya Talata, ya mika masa wani sako kai tsaye daga Paparoma Francis. Turkson, wanda ya fito daga Ghana, ya ce ya tattauna da Kiir kan bukatar kawo karshen wannan tashin hankalin a Sudan Ta Kudu.

Ya ce Kiir ya ba shi tabbacin cewa har yanzu ya himmantu ga maido da zaman lafiya a kasar. Cardinal din ya ce yana so ya gana da Machar, to amma tsohon jagoran 'yan tawayen ya arce daga Juba, jim kadan da barkewar fadan kuma ya na zauna ne a wani boyayyen wuri a Sudan Ta Kudun, a cewar mai magana da yawunsa.

Kiir na matukar adawa da wani yinkuri na kungiyoyin yanki, da Kungiyar Gwamnatocin Kasashe ta kawo Cigaba IGAD da kungiyar Tarayyar Afirka na girke sojoji a Juba don kawo kwanciyar hankali a babban birnin kasar su kuma shiga tsakanin sojojin da ke biyayya ga Shugaban kasar da masu biyayya ga Machar. Turkson ya ce Shugaban kasar ya ce a shirye ya ke ya gana da Machar.

.

XS
SM
MD
LG