Wata dalibar jami’a, ‘yar shekaru ishirin da shida, Hajah Awah wadda ta rasa danginta uku a harin da kungiyar Boko Haram ta kai a garin Mora dake kan iyaka da Najeriya shekaru biyu da suka shige, ta ce a matsayinta na wadda hare haren ya shafa, tayi mamaki zargin rudunar sojin Kamaru da kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty tayi, da keta hakin bil’adama a yaki da kungiyar Boko Haram, da tace, babu abinda suke yi sai kisa da fyade da sata.
Tace, tana gani kungiyar Amesty International tana da wani mugun nufi na durkusar da Kamaru, domin Kamaru da Najeriya da Chadi da kuma Nijar dukansu suna yaki da Boko Haram, sai dai kungiyar tana sha’awar buga rahotannin keta haki a kasar Kamaru kawai. Tace kamata ya yi kungiyar Amnesty ta bayyanawa duniya irin akuba da mutuwa da jama’a ke yi a hannun mayakan kungiyar Boko Haram, da kuma kokarin da sojojin Kamaru ke yi na ceton rayukansu.
Enenezer Akanga, wani ma’aikacin tashar talabijin ta kasar Kamaru da ya kware wajen kai rahotannin hare haren kungiyar Boko Haram yace, irin wadannan rahotanni zata kashe guiwar sojojin dake kokarin samar da zaman lafiya a kasar da ta rasa rayuka da kaddarori a harin ta’addanci.
Kasa kamar Kamaru ba zata yi yaki da ta’adanci ba, sai kungiyar amnesty tayi tunanin abinda zata iya yi shine rubuta rahotanni cewa gwamnati tana kuntatawa mayakan Boko Haram. Kungiyar Amnesty ta taba rubuta rahoto tana allah wadai da kashe 'yan kasar Kamaru da kungiyar Boko Haram ke yi? Kungiyar Boko Haram tana da 'yancin kashe 'yan kasar Kamaru? Menene yasa basu cewa komi idan boko haram ta kashe 'yan kasar Kamaru sai dai suyi ta babatu idan sojojin Kamaru suka kashe mayakan kungiyar Boko Haram?
Wani masanin ilimin halayyar bil’adama da zamantakewa Emannuel Ossomba, yace kungiyar Amnesty tana yin aikinta ne kawai na taimakawa wajen kare mutanen da mai yiwuwa suna wahaka a gidan yari.
Aikinsu kawai suke yi. Suna Magana cewa Kamaru ta kiyaye dokokin kasa da kasa. Amnesty na cewa, wurin da ake tsare da mutanen bashi da kyau.
Rahoton da kungiyar amnestay ta buga ranar sha hudu ga watan nan na Yuli da taken “kyakkyawar Manufa, hanyar da bata dace ba, na nuni da cewa, sama da mutane dubu daya da ake zargi da goyon bayan Kungiyar Boko haram da aka kama suna zaune a cikin wani yanayi da bai kamata ba, ana kuma gasawa wadansu akuba.