Arsenal Ta Amince Da Tayin Fam Miliyan 4.45 Kan Lucas Perez

Kungiyar kwallon kafa ta Everton, ta cimma yarjejeniya da kungiyar Barcelona, kan sayen dan wasan bayanta Yerry Mina, mai shekaru 23 da haihuwa akan kudi fam miliyan 28.5 na tsawon shekaru biyar.

Har ila yau Kungiyar ta Everton, ta shaida wa Manchester united, cewa tana bukatar dan wasan bayanta Chris Smalling, ko kuma Victor Lindelof, dan shekaru 24, a duniya in har kungiyoyin biyu basu daidaita kan sayen dan wasan Manchester united ba.

Manchester United, na cigaba da shirye shiryenta na neman dan wasan Leicester, Harry Maguire mai shekaru 25, da tunanin kuma cewa za su biya kulob din kudi mafi yawa kan na kasar Ingila.

Chelsea na da sha'awar sayen dan wasan Crystal Palace, dan kasar Ivory Coast, Wilfried Zaha, mai shekaru 25, bayan Tottenham ta fita daga zawarcin sa, Sabon Kocin kungiyar Chelsea, Sarri yace kungiyar a shirye take ta sayar da mai tsaron ragarta Courtious, ga kungiyar Real madrid in har yana bukata.

Wakilin dan wasan tsakiya na Arsenal, Aaron Ramsey's ya musanta rade radin da ake yi na cewar dan wasan yace sai an bashi kudi fam dubu 300 a sati in har ana son ya sake sabunta kwantirakinsa a kungiyar, dan wasan dai yana da sauran yarjejeniyar kwantirakin shekara guda a kungiyar.

Arsenal ta amince da tayin fam miliyan 4.45 daga kungiyar Sporting Lisbon domin sayar da dan wasanta Lucas Perez mai shekara 29

Mousa Dembele, dan kasar Belgium mai shekaru 31 ya ki amincewa da tayin da aka yi masa na komawa kungiyar Inter Milan daga Tottenham.

Your browser doesn’t support HTML5

Arsenal Ta Amince Da Tayin Fam Miliyan 4.45 Kan Lucas Perez