Arrangama Da Turmutsutsi Bayan  Wasan Kwallon Kafa Sun Sabbaba Mutuwar Mutane 56 A Guinea – Hukumomi

Wani filin kwallon kafa a Guinea inda turmutsutsin ya awku

Mutane 56 sun mutu kuma da dama sun jikkata sakamakon turmutsutsin da ya afku a wani filin wasan kwallon kafa a kudancin Guinea, biyo bayan arangama tsakanin magoya bayan kungiyoyin kwallon kafar, kamar yadda gwamnatin Guinea ta bayyana a yau Litinin.

Hukumomi na gudanar da bincike domin gano wadanda suka haddasa turmutsutsin a jiya Lahadi, a cewar sanarwar da ministan sadarwa Fana Soumah ya karanta a tashar talabijin din kasar.

Cikin wadanda al’amarin ya rutsa dasu akwai kananan yara da dama a cewar wata kafar yada labaran kasar da gamayyar jam’iyyun siyasa.

Turmutsutsin ya afku ne da maraicen jiya Lahadi a filin wasa na birnin Nzerekore yayin wasan karshe na wata gasar da ake buguwa a kasar tsakanin kulub din Labe da takwaransa na Nzerekore domin karrama jagoran sojin kasar, Mamadi Doumbouya, kamar yadda firai ministan Guinea Amadou Oury Bah ya wallafa a shafinsa na X.

“Yayin turmutsutsin, an samu mutanen da al’amarin ya rutsa dasu,” a cewar Bah, ba tare da yin karin bayani ba. Hukumomin yankin na kokarin dawo da doka da oda a yankin, a cewarsa.

Kafafen yada labaran yankin sun bada rahoton cewar jami’an tsaro sun yi kokarin yin amfani da hayaki mai sa hawaye wajen dawo da doka da oda bayan yamutsin daya biyo bayan takaddama akan bugun fenariti.

“Takaddama akan bugun fenariti ya fusata magoya baya wadanda suka rika jifa da duwatsu. Wannan ne ya janyo jami’an tsaro yin amfani da hayaki mai sanya hawaye,” kamar yadda Media Guinea, wata kafar yada labaran yanar gizon kasar, ta bada rahoto. Ta kara da cewar galibin wadanda suka mutun kananan yara ne yayin wadanda suka jikkata dake samun kulawa a wani asibitin yankin ke cikin mawuyacin hali.

-AP