AREWA A YAU: Yadda Farashin Kayan Masarufi Ya Karu Da Kimanin Kashi 50%

Nasiru Adamu El-Hiyaka Lokacin Kan Hanyar Kaduna Zuwa Abuja

Sabon shirin AREWA A YAU zai duba shawara ga jama'a a gida su rika taimakawa juna yayin da lamuran tattalin arziki ko kuncin rayuwa ke karuwa a jihohin arewa, 'yan kananan sana'o'i na yau da kullum za su taimaka.

Mata na iya ba da gudunmawa wajen taimakawa rayuwar gidajen su ta hanyar sana'o'i da za'a iya aiwatarwa daga cikin gida.

Bayanai na nuna muhimman kayan masarufi sun kara farashi da kimanin kashi 50%. Hakan ya fi zama damuwa don ya shafi kayan abincin da ake nomawa a yankin arewa.

A tarukan da mata kan yi a Abuja don duba hanyoyin taimakawa kai don amfanin abokan zaman su maza da kuma yaran su, Hajiya Adamawa Mai Agogo ta kafa wata kungiya da ke karfafawa mata gwiwa su rage burin rayuwa da tallafawa da ta su basirar don samun fahimtar juna.

Saurari rahoton a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

AREWA A YAU: Yadda Farashin Kayan Masarufi Suka Karu Da Kimanin Kashi 50%