AREWA A YAU: Shawarwari Kan Sassauta Kuncin Tattalin Arziki A Arewacin Najeriya, Agusta 30, 2023

Nasiru Adamu El-Hiyaka Lokacin Kan Hanyar Kaduna Zuwa Abuja

ABUJA, NIGERIA - A shirin Arewa A Yau na wannan makon mun duba shawarar dattawa kan yadda za a sassauta kuncin tattalin arziki a yankin Arewa da kuma yadda aka buda burtali a tsakiyar Arewa maso Gabas don bai wa makiyaya da manoma hakkin su.

Hakika duk wanda ya yi yawo a yankin Arewa a ‘yan kwanakin nan zai ga yadda akasarin talakawa su ke gwagwarmayar neman abinci sau uku a wuni inda wasu kan koka cewa a kan samu kwanaki ba a dora tukunya ba.

Saurari shirin da Nasiru Adamu El-Hikaya ya gabatar:

Your browser doesn’t support HTML5

AREWA A YAU: Shawarwari Kan Sassauta Kuncin Tattalin Arziki A Arewacin Najeriya, Agusta 30, 2023.mp3