Babachir Lawal yayin taron jiga-jigan APC na Adamawa a nan Abuja inda suke bijerewa batun zaben fidda gwani ta hanyar wakilai wato delegates a jihar, ya ce idan jam’iyyar APC bata yi takatsantsan ba, za ta iya rasa jihar Adamawa a zaben 2019.
"Yanzu haka mutane hudu sun sayi fom din tsayawa takarar Gwamna a jam’iyyar APC a Adamawa, idan aka hana uku tsayawa takara hakan zai iya janyo wasu su ki yiwa jam’iyya aiki ko su balle," inji shi Babachir.
Da wakilin sashen Hausa ya tambaye shi ko yana neman tsayawa takara ne? Sai ya ce, ‘A’a, bana neman komai don na tsufa na fi shekarun gwamna,"
Ya ce ci gaba da cewa idan uwar jam’iyya ba ta yarda da bukatarsu ba za su fita su zabi Shugaba Muhammadu Buhari amma ba za su zabi gwamna ba.
Domin a cewarsa, gwamna Bindo Jibrilla in banda wani kwalta a kan hanya babu abun da ya tabukawa jihar.
Da yake mayar da martani kan wannan batu, kwamishinan labarai na jihar Adamawa Sir. Joe Ahmed, ya ce dokar tsarin mulkin jam’iyyar APC ce ta fitar da hanyoyin da za bi a don fidda gwanaye. Ya ce shugabannin jam’iyyar ce ta dauki wannan matsayin ‘yar tinke sannan kuma kiyyaya da hassada ce zasu sa mutum ya shiga jihar Adamawa ya ce bai ga komai a kasa ba.
Saurari cikakken rohoton Hassan Maina Kaina
Your browser doesn’t support HTML5