APC Tayi Taron Jihohin Arewa Ta Tsakiya Da Nufin Shawon Kan Matsalolinta Kafin Zaben Badi

Taron Jam'iyyar APC a Abuja.

Jam’iyyar APC Mai Mulki a Najeiriya na gudanar da tarurruka daban daban da nufin kara dinke duk wata barakar dake tsakanin yayanta kafin babban zaben na badi.

A kan haka ne ma APC ta gudanar da wani taron masu ruwa da tsaki a APC a jihohin Arewa Maso Tsakiyar Nigeria.

Mataimakin Shugaban APC na Nigeria mai kula da jihohin arewa maso tsakiya Alh. Mu’azu Bawa Rijau yace suna da tabbacin shawo kan duk wata 'yar matsala kafin babban zaben na badi.

A nashi gefen Mataimakin Gwanan jihar Neja Alh. Ahmed Muhammad Ketso yace zasu tunkarin zaben tamkar yaki.

Wasu daga cikin mahalarta wannan taro da suka hada da shugaban matasan APC na jihar Neja da kuma shugaban masu fama da nakasa a APC a jihar Neja sun yi fatan za a yi tafiyar dasu dari bisa dari.

Haka zalika da dama daga cikin mahalarta wannan taro sun yi fatan gwamnatin APC karkashin Shugaban Buhari zata kammala ayyukan da ta faro a jihar Nejan ciki har da tashar Ruwan Baro.

Saurari rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

APC Tayi Taron Jihohin Arewa Ta Tsakiya Da Nufin Shawon Kan Matsalolinta Kafin Zaben Badi