Alhaji Hassan Jika Ardo shugaban jam'iyyar APC a jihar Taraba ya zargi gwamnan jihar da yin kama karya tare da bada misali wai ana muzgunawa wasu ma'aikata a jihar da kuma sauya masu wuraren aiki sakamakon zuwansu kotu domin sauraren shari'ar da ake yi akan kujerar gwamnan.
Haka ma yace ana yiwa wasu ma'aikatan gidan rediyon jihar bisa zargin cewa suna caccakar manufar sabuwar gwamnatin a dandalin zumunta na Facebook.
Akwai kuma korar wani tsohon dan jarida kuma tsohon hadimin tsohon mukaddashin gwamnan jihar Alhaji Garba Umar, wato Aaron Atimas da gwamnan ya yi. Bugu da kari gwamnatin jihar ta kuma fitar dashi daga cikin gidan gwamnatin da yake haya yau fiye da shekaru goma sha biyar alatilas.
Alhaji Ardo yace mutane su lura da kyau. Abun da suke fadi ya faru ne a zahiri. Yace misali a jihar mutum bashi da 'yancin ya fadi ra'ayin kansa ko ya zabi abun da yake so. An sake wa mutane wuraren aiki saboda fadin ra'ayoyinsu.
Shi ma Mr. Aaron Atimas yace gwamnatin ta bashi wa'adin ficewa cikin gaggawa daka gidan da yake yanzu. Yace a wurin da yake zaune su da suka bar aiki sun fi goma amma ba'a taba sauran ba sai shi. Akwai wasu kuma a wasu gidajen amma ba'a yi masu ba sai shi kadai. Yace da sassafe aka je gidansa da misalin karfe biyar domin bashi takardar fita daga gidan. Yace mulkin danniya ke nan ba na dimokradiya ba.
A martanin da ya bayar gwamnan jihar ta bakin mai bashi shawara ta fuskar harkokin siyasa Alhaji Abubakar Bawa ya musanta zargin. Yace a matsayinsu na gwamnati ko an yiwa wani canjin wurin aiki ko menene ma basu sani ba. Dangane da fitar da Mr. Atimas daga gidansa sai yace basu san da batun ba kuma watakila maganar tsakninsa ne da masu kula da gidajen.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.
Your browser doesn’t support HTML5