Ana ci gaba da dambarwa game da zaben majalisun kananan hukumomin jihar Taraba, a bayan da gwamnatin jam'iyyar PDP mai mulki ta fito ta kara wa'adin shugabannin rikon da ta nada a yankunan.
Jam'iyyar APC a Jihar ta Taraba, ta zargi gwamnatin jam'iyyar PDP da laifin jan kafa wajen gudanar da zabubbukan na kananan hukumomi. Shugaban APC a jihar, Hassan Jika Ardo, yayi Allah wadarai da kara ma kantomomin na kananan hukumomi wa'adi yayin da suke gaban kotu su na kalubalantar matakan na gwamnatin Taraba.
Yace idan suka samu nasara a shari'ar da suke yi, to lallai kantomomin da PDP ta nada a kananan hukumomin zasu mayarda duk kudaden da suka karba, ciki har da na albashi, sannan duk matakan da suka dauka zasu kasance na haramun.
Sai dai kuma, kakakin gwamna Darius Ishaku na Jihar Taraba, Mr. Sylvanus Giwa, yace idan lokacin zaben kananan hukumomi yazo, zasu gudanar da shi. Yace babu wanda zai ingiza su su gudanar da zaben har sai lokacin yinsa yayi.