Jam'iyyar ta APC ta ce ta fi son Jonathan din ma ya tsaya takara don zai fi saukin kayarwa a zabe.
WASHINGTON, DC —
Babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya, APC, ta musanta zargin da jam'iyyar PDP mai mulki ta yi cewar APC tana ta kulle-kullen ganin cewa shugaba Goodluck Jonathan bai tsaya takara a zaben shekarar 2015 ba.
Mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa, Aminu Bello Masari, ya fadawa wakilin Sashen Hausa, Hassan Umar Tambuwal a birnin Ibadan cewa ba zasu daina kushe lamirin shugaban ba, domin ta haka ne zasu iya nunawa duniya irin gazawarsa tare da tabbatar da cewa duk wanda jam'iyyarsu ta tsayar ya samu nasara a 2015.
Tsohon ministan babban birnin tarayya, Nasir El-Rufa'i, wanda shi ma jigo ne a jam'iyyar ta APC, yace su kam sun ma fi kwadayin ganin jam'iyyar PDP ta tsayar da shi shugaba Goodluck Jonathan yayi mata takarar shugaban kasa domin kuwa zasu fi jin dadion kayar da shi a lokacin zaben.
Yace shugaba Jonathan ba ya da wani abinda zai iya tinkaho da shi a zaman ci gaban da ya kawo ma Najeriya in ban da tashin hankali da rashin tsaro da kuma mummunar satar dukiya.

Your browser doesn’t support HTML5