Jam'iyar APC mai mulki a Najeriya, ta ce duk wani mai korafi dangane da zabukan mazabu da aka yi na gama-gari domin zaben shugabannin jam'iyar a sassan kasar.
Sakataren jam’iyyar na kasa Mai Mala Buni wanda ya bayyana hakan ya ce jam’iyyar za ta yi wa kowa adalci.
A cewarsa ayyukan da kwamitocin za su yi, akwai tabbacin za su warware kowace takaddama da ta taso.
"Duk inda jam’iyyar ta tura a yi zabe a jihohi 36 na kasar ta kafa kwamiti da zai saurari korafe korafe idan sun taso. Kwamitin karban koke koke bashi ba ne kwamitin zabe." Inji Sakataren na APC.
Ya kara da cewa yanzu babu wata rigima da ta taso cikin jam’iyyar da ta fi karfinta.
Daga cikin masu korafin, akwai wasu manyan jam’iyyar da suka hada da gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha da ke cewa zaben bai tafi yadda ya kamata ba.
Har ma sun yi barazanar ficewa daga jam’iyyar matukar ba’a soke zaben da aka yi a yankunan su ba.
Sanata Suleiman Hunkuyi daga jihar Kaduna shi ma na daya daga cikin wadanda suka yi korafi akan rashin ingancin zaben.
A cewarsa, bai yarda da zaben ba, domin babu Dimokradiya cikinsa inda ya kwatanta shi a matsayin "zalunci ne tsantsa."
Ga cikakken rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya:
Your browser doesn’t support HTML5