Jamiyar ta bayyana cewa hakan baya rasa nasaba da zaben cike gurbi da na kananan hukumomi dake kara matsowa.
Jam'iyar ta APC ta koka ne bayan kama kama wani jigo a jam’iyar Alhaji Abubakar Dan Tabawa ranar asabar lokacin da ya je kai tallafi ga wadanda ambaliyar ruwa yayi musu barna a garinsu.
Da yake maida martini game da zargi, Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Zamfara, Abubakar Muhammed Daura ya bayyana cewa, dukan matakan da hukumumi su ke dauka suna yi ne isa dalilan tsaro.
A nashi bayanin, Kakakin rundunan Yan Sanda ta jihar Zamfara SP Shehu Muhammed, yace “ hakin tabbatar da zaman lafiya na cikin gida ya taraya ne a wuyan rundunan 'yan sanda, wadda ta ke kokarin ganin an kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Saboda haka abinda take yi a jihar Zamfara ba kuntatawa kowa bane,aikinta take yi kamar yadda tsarin mulki ya tanada na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
SP Shehu ya kara da cewa, “suma masu wannan zargin, na tabbatar da babu tsaro a jihar Zamfara, inda suke zaune suna wannan zargin da ba zasu yi shi ba. Aikin jami’an tsaro wanda tsarin Mulki ya yadda dashi, shine kame duk wanda ake zargi ko ake tuhuma ko ya aikata laifi ko zai aikata ko kuma yana cikin aikatawa."
Saurari cikakken rahotan Sani Shu’aibu Malumfashi:
Your browser doesn’t support HTML5