Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Jimamin Rasuwar Tsohon Minista Inuwa Abdulkadir


Inuwa Abdulkadir
Inuwa Abdulkadir

A Najeriya ana ci gaba da jimamin rasuwar tsohon minista a jihar Sokoto Alhaji Inuwa Abdulkadir wanda ya rasu a safiyar yau Litinin.

Har yanzu dai ba a tabbatar da sanadiyar mutuwar ba.

Tsohon sanata kuma makusancin marigayin Shehu Sani, yana daya daga cikin mutane na farko da suka tabbatar da faruwar lamarin kan shafukan sada zumunta.

Tuni sauran abokan tsohon ministan suka karade shafukan sada zumunta wajen nuna alhininsu akan mutuwar tasa.

Alhaji Inuwa dai shi ne mataimakin shugaban APC a arewa maso yammacin Najeriya kafin a rusa shugabancin jam'iyyar a kwanan nan.

Kafin rasuwarsa, ya taba zama ministan wasanni a gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan, ya kuma taba zama kwamishinan shari'a na jihar Sokoto karkashin gwamna Aliyu Wammako.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG