Bayanai daga Najeriya na kara nuni da cewa ana ci gaba da samun baraka a wasu daga cikin jihohin da jam’iyyar APC ke jagoranta, tun bayan da aka kammala zaben mazabu a duk fadin kasar.
Jaridar Daily Trust a shafinta na yanar gizo a yau Lahadi ta ruwaito cewa an samu baraka a jihohin Kwara, Oyo, Kogi, Kano baya ga wasu jihohi.
Zabukan har ila yau, sun haifar da sabani a jihar Imo inda gwamnan jihar Rochas Okorocha ya kalaubalanci sakamakon zaben.
Masu lura da al’amura na ganin wannan matsala da jam’iyyar ke fuskanta a kusan daukacin kasar ka iya zama mata kalubale, lura da cewa ana tunkarar zaben gama gari a shekara mai zuwa.
Rahotanni sun ce tuni aka samu bangarewa a wasu jihohi a tsakanin ‘ya’yan jam’iyar, misali jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, jam’iyyar ta bangare zuwa gida biyu a jihar Kwara.
Akwai bangaren da shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki yake jagoranta, yayin da Ministan yada labarai da al’adu, Lai Muhammed, ke jagorantar daya bangaren.
Haka ma lamarin yake a jihar Kogi, inda jam’iyyar ta bangare biyu acewar jaridar.
Babban Sakataren jam’iyyar ta APC, Mai Mala Buni, a wata hira da ya yi da Muryar Amurka a makon da ya gabata, ya ce akwai kwamitin shigar da korafi da jam’iyyar ta kafa a kowacce jiha.
Ya yi kira ga daukacin masu korafi da su garzaya zuwa wadannan kwamitoci domin gabatar da korafe-korafensu.
Haka zalika, wasu manyan jami'an jam'iyyar da Muryar Amurka ta zanta da su, sun ce irin wannan rikici ba sabon abu ba ne, kuma za su sasanta kansu komin dadewa.