Yanzu haka ma tuni aka shigar da karar gwamnan jihar Adamawa a gaban kotu bisa zargin bashi da takardun kammala makarantar sakandare, batun da ya bude wani shafi a dambarwar siyasar jihar.
Koda yake kawo yanzu sunan gwamnan jihar Adamawan ne Sanata Muhammadu Umaru Jibrilla Bindo, jam’iyar ta APC taka mikawa hukumar zabe, INEC, don gudun kurewar lokaci, da alamun da sauran rina a kaba, biyo bayan garzayawan da wata kungiya ta Global Integrity Crusade, ta yi zuwa kotu game da batun takardun gwamnan, yayin da daya bangaren suma sauran yan takarar da suka tsaya da gwamnan ke cewa ba zata sabu ba wai bindiga a ruwa.
Tuni ma Dakta Mahmud Halilu Ahmad, wato Modi, dake cikin yan takarar ya rubutawa uwar jam’iyar APC wasikar ankararwa dangane da wannan badakalar da ake zargin gwamnan.
Suma dai yan kungiyar Black-Cap dake tare da bangaren Mallam Nuhu Ribadu, har jerin gwano suka yi zuwa Majalisar Dokokin jihar na neman a gudanar da bincike.
To wai ko me gwamnan jihar Adamawan ke cewa game da wannan batu? Kwamared Ahmad Sajo shine kwamishinan yada labarum jihar yace, su ko a gyalensu.
Kamar Adamawa a makwabciyar tama wato jihar Taraba, ana ci gaba da kai ruwa rana a tsakanin wasu yan takarar gwamnan da kuma wanda tun farko aka ayyana cewa shi ya lashe zaben fidda gwanin Sani Abubakar Danladi, wanda kuma yanzu an zura ido aga yadda zata kaya.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Your browser doesn’t support HTML5