APC Da PDP Na Kai Ruwa Rana

Nigeria Decides Promotion Banner

Ga dukkan alamu kace-nacen da ake yi a Najeriya tsakanin mai magana a madadin jam'iyyar APC da mai mulki da na jam'iyyar PDP mai adawa ya kazance

.An ruwaito Sakataren yada labaran APC na kasa, Lai Mohammed na gaya ma PDP cewa au ta daina kuka ta sake fasalinta, au ta dusashe.

Wannan na faruwa ne bayan da PDP ta zargi Shugaba Muhammadu Buhari da ci gaba da yin kalamai marasa amfani kan tattalin arzikin Najeriya, wadanda a cewar PDP su na tsorata masu niyyar saka jari a Najeriya.

Lai Mohammed ya ce PDP ce ta janyo ma kanta faduwa.

To amma Olisa Metuh, Sakataren yada labaran PDP na kasa, ya ce ya kamata Shugaba Buhari ya bullo da nasa irin tsare-tsaren na yadda za a gyara abin da Shugaban ke kira durkusasshen tattalin arziki, a maimakon ya yi ta sukar gwamnatin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan.

Metuh ya ce gwamnatin Buhari ba ta da alkiblar manufofi da kuma azanci kan yadda za a bunkasa tattalin arzikin Najeriya a kuma dora kan cigaban da PDP ta samar cikin shekaru 15 da su ka gabata.

A bangare guda kuma, Lai Mohammed na cewa yadda PDP ta yi ta lalata cibiyoyin gwamnati da kuma bakanta kowa in banda ita kadai, ba zai haifar ma jam'iyyar komai ba illa, kaicon siyasa.