Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Filato: Kotu Ta Kori Karar Da PDP Ta Kai


Alamar hukumar zabe ta INEC
Alamar hukumar zabe ta INEC

Jam'iyyar PDP ta sha kaye a shari'ar da aka yanke kan zabe a jahar Filato, wadda ta tabbatar da nasara ga jam'iyyar APC.

An kori karar da jam’iyyar PDP ta kai ta zargin magudi a zabukan da aka gudanar a jahar Filato, inda ta ke tuhumar Samuel Lalong da jam’iyyar APC da coge a zabukan.

Wakiliyar Sashin Hausa a shiyyar Filato, Zainab Babaji ta ce an shafe sa’o’I biyar ana karanta bayanan bangarorin biyu – wato masu kara da wadanda ake kara – a kotun cikin tsauraran matakan tsaro. Mai Shari’a Justin Candida y ace masu karar sun kasa gabatar da gamsassun bayanai da shaidu na zargin da su ke yi, abin da ya say a yi watsi da karar tare da umurta masu karar da su bai wa wadanda su ka zarga Naira 50,000 kowanne.

Ta yi hira da daya daga cikin ‘yan jaridar da su ka hallara mai suna Mohammed Shitu, wanda ya kara da cewa kotun ta ce shaidu 10 da bangaren PDP ya kawo, wadanda su ka yi bayanai, ba za a iya amfani da bayanansu ba saboda su kansu sun ba da bayanai masu karo da juna a kotun – don haka bayanan nasu sun zama jita-jita.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG