Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

INEC Ta Shirya Gudanar da Zaben Cike Gurbin Sanata a Borno


INEC
INEC

Hukumar zaben Nakeriya ko INEC ta ce ta gaba kimtsawa domin ta gudanar da zabencike gurbin sanata da ya rasu a jihar Borno.

Zaben da za'a yi ranar Asabar mai zuwa zai cike gurbin da Sanata Ahmed Zanna mai wakiltar Borno ta tsakiya ya bari biyo bayan rasuwarsa.

Hukumar zaben reshen jihar Borno tace ta karbi kayan aiki tare da horas da ma'aikata da zasu gudanar da zaben ranar 31 ga wannan watan Oktoba.

Samuel Usman Madaki shugaban hukumar na jihar Borno yace sun gama duk shirye shiryensu dangane da zaben. 'Yan takara takwas ne zasu fafata.

Ana kyautata zaton adawa zata yi zafi a zaben saboda rashin jituwa dake tsakanin 'yan jam'iyyar APC dake mulkin jihar. Yanzu suna taken cewa Borno ta fi jam'iyya. Zasu zabi dan takaran da ya cantanta ba jam'iyya ba saboda wai wasu tsiraru sun yi kane-kane a APC.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:07 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG