Shugaban kasar Nijar ya ce gwamnati ta yi yunkurin murkushe wani juyin mulki, wadanda suka kitsa wannan danyen aiki sun so su mayar da hannun agogo baya a game da mulkin demokaradiyya da jama’ar kasar suka zabar ma kan su, ta hanayar anfani da makaman da al’uma ta basu amana domin aikin tsaro.
Masu hannu a wannan yunkuri sun tsara yi wa fadar shugaban kasar barin wuta da jiragen sama da suka jibge a tsawon makonni da dama domin biyan bukatar da suka sag aba, alhali shugaban ya umurce su tun da dadewa cewar su aika wadannan jirage zuwa yankin diffa domin karfafa matakan tsaro inda ‘yan uwan su kuma abokan aikin su ke matukar bukatar wadannan kayan aiki domin fatattakar ‘yan boko haram. Shugaban ya kara da cewa wadannan sojoji sun cuta ma abokan aikin su ne.
Da yake cigaba da bayani, shugaban ya bayyana cewar Allah ne ya tona asirin wadanda suka kulla wannan ta’asa shiyasa suka kasa samun nasara, kuma an gano su kaf kuma sun shiga hannu sai guda daya ne tak da ya arce, kuma kawo yanzu ana nan ana cigaba da binciko sauran duk wadanda ke da hannu a lamarin domin gurfanar da su gaban kuliya.
A cewar editan jaridar lebaniman Musa Aksar ya yi Karin bayanin cewa bincike ya nuna masu cewar anso a yi wanna juyin mulki da farko abin ya ci tura sai suka sake shiri yayinda suka yi yinkurin yin hakan a yau alhamis.
A cikin wadanda aka samu da hannu cikin wanna yunkurin juyin mulki sun hada da mai mukamin janar Salu Suleiman, da laftanar kanar Idi Na Hauwa kwamandan filin jiragen soji, da kuma laftanar kanar Nare Mai Doka wanda ke rike da bataliyar tilaberi da kuma wani kwamanda mai suna Ahmadu da kuma kyaftin Isihi da laftanar Hambali