Kamfanin Twitter ya aikawa wasu mutane da kamfanoni dake da shafin Twitter gargadi, na cewa masu kutse da gwamnati ke ‘daukar nayinsu nakokarin satar bayanan sirrinsu, Twitter tace wannan shine lokaci na farko da ta fara aikawa mutanen da aka yi kokarin kaiwa hari sako.
Sanarwar dai ba ta tabbatar da cewa masu kutsen sun sami nasarar satar bayanan mutanen ba, amma an nuna cewa an kaiwa wasu mutane kalilan hari, wato ba dukkan mutanen da ke da shifin aka kaiwa ba.
Haka zalika sanarwar bata fadi yadda aka kai harin ba ko bayar da bayanan maharan ba, har yanzu dai ana bincike akai.
Sanarwar dai ta kawo karin damuwa kan kutse da ake a yanar gizo, wanda wani lokaci manyan kamfanoni ke ‘daukar nauyi, ma’aikatocin gwamnati da kasuwanni da kafofin yada labarai duk na fuskantar ire iren wannan kutse.
Kamfanin Coldhak da yake mai zaman kansa yace ya samu wannan sanarwar ne ranar Juma’a, inda aka gaya masa masu kutsen na kokarin samun bayanan sa kamar su adireshin email da lambobin waya da gano adirshin din inda mutum yake. Wanann kamfani dai da sauran mutanen da akayi kokarin yiwa kutse basu da masaniyar dalilin da yasa aka kai musu harin.
Google da Facebook suma sun fara aikawa mutane sanarwa a duk lokacin da suka fuskanci ana kokarin kai musu irin wannan hari.