A ci gaba da tattaunawar da muka fara satin da ya gabata akan yadda wayar hannu da shafukan yanar gizo ke shafar rayuwar matasa, jama'a da dama sun tofa albarkacin bakin su akan yadda su da kansu suka fahimci yadda lamarin ke shafar rayuwar su ta yau da kullum.
A kasashen da suka ci gaba, masana sun dukufa wajan nemo hanyar rage yawan mayar da hankali akan wayar hannu da yawaita ziyartar shafukan sada zumunta na yanar gizo, ganin yadda a lokuta da dama jama'a kan tsallaka titi ba tare da sun sani ba. wasu kuma kan yi karo da juna domin hankalin su duk yana kan waya.
A shekarar data gabata, kafar sadarwar talabijin ta CNN, ta nuna bidiyon wata mata da ta fada rami har ta sami raunika a sakamakon tana tafiya amma hankalinta na kan wayar hannu, an sami ma'aurata da dama da basa zaunawa su tattauna da juna a cikin gidajen su domin kowa na kan waya. iyaye basu da lokacin zama da 'ya'yan su domin fahimtar yanayin da suke ciki duk saboda wannan fasahar zamani.
Abokai kan manta suna tare da juna domin kowa ya dukufa wajan chatting ko kuma kallon hotunan wata duniyar daban, anya wannan fasaha baza tai wa zumunci karan tsaye ba kuwa?
ku biyo mu sati mai zuwa idan Allah ya kaimu domin ci gaba da tattaunawa akan wannan lamari amma kafin lokacin muna so ku bayyana mana ra'ayoyin ku akan yawaita amfani da wayar hannu domin shiga shafukan yanar gizo, ta wacce hanya wannan lamari ke shafar rayuwar ku?