Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, ya gana da shugaban Najeriya Bola Tinubu a yau Talata a fadar gwamnati dake Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.
Washington DC —
Kasar na cikin jerin kasashe a yammacin Afirka da Sakataren ya kai ziyaran aiki.
Ganawar na cikin wani yunkuri na kara bunkasa hulda, samar da hadin kai da bunkasa tattalin arziki tare da wasu muhimman kasashen Afirka, yayin da rikice-rikice suka dabaibaye duniya.
Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya ce Blinken zai kuma ziyarci kasar Angola, wadda ta sauya daga yaki zuwa dimokradiyya, kuma ta taka muhimmiyar rawa wajen shiga tsakani domin kawo karshen tashe tashen hankula a jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo.